Matar da mijinta ya daure ta a daki ta rasu a Kano

0
139

Sadiya Amin, matar da mijinta ya daure ta a daki tsawon watanni ta rasu a asibitin da aka kwantar da ita.

A daren Lahadi ne daya daga cikin masu jinyarta tare da taimaka mata, a karkashin Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo Foundation, Musa Abdullahi Sufi ne ya sanar da rasuwar ta shafinsa na Facebook.

Ana zargin mijin marigiyar ya kulle ta a daki cikin tsananin rashin lafiya, bai kai ta asibiti ba, sai dai ya ba ta koko da naman hazbiya kamar yadda muka ba ku labari a kwanakin baya.

Daga bisani mahifiyarta da ta kai ziyara inda take da dawo da ita Kano, bayan ta ga halin da ta ke ciki.

 

Kwnanaki kadan da kawo ta Kano, mahaifinta ya rasu, wanda cewar Abdullahi Sufi ya ce na da alaka da ganin halin da ’yar sa ta shiga.

Fitacceen dan gwagwarmayar ya ce ba za su kyale lamarin ba, sai sun dauki matakin da ya dace wajen bi wa marigayiyar hakkinta.

 

“Yanzu za mu dukufa wajen nemo wa Sadiya hakkin ta wajen wannan miji da ya zalunce ta,” in ji shi.

 

Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi hattara da wasu kungiyoyi da mutane da ke neman tallafi da sunan marigayiya Sadiya.