Za a fara hako mai a Arewa ranar Talata

0
106

A karon farko Najeriya za ta fara hako danyen mai daga rijiyoyin mai da aka gano a yankin Arewacin kasar, a jihohin Gombe da Bauchi a ranar Talata.

Majiyoyi masu tushe a kamfanin mai na NNPC sun tabbatar da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci kaddamar da aikin hako danyen mai na farko a Arewa a Rijiyoyin Mai masu lamba 809 da 810 da ke jihohin Bauchi da Gombe.

Majiyarmu ta ce Buhari wanda zai kaddamar da aikin tare da Minista a Ma’aikatar Albarkatun Mai, Timipre Sylva, ya zaku a fara aikin kafin wa’adin mulkinsa ya kare.

Wannan shi ne karon farko da za a hako mai daga yankin Arewacin Najeriya tun bayan da aka gano arzikin mai da yawansa ya kai na kasuwanci a yankin, kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Majiyoyin sun bayyana cewa hako danyen man daga Arewa shi ne babban aikin hakar mai na farko a Najeriya bayan sauye-sauyen da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi a bangaren mai.

Kafin wannan, an dakatar da aikin neman danyen mai a Jihar Borno saboda matsalar rashin tsaro.

A 2016 NNPC ta kaddamar da aikin neman arzikin mai a yankin Arewacin Najeriya wanda ya kai ga ganowa a jihohin Bauchi da Gombe da Neja da kuma Borno.