Aisha Buhari ta yi kunshi mai tambarin Tinubu

0
158
Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bullo da sabon salon kunshi mai dauke da tambarin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu.

Fitar hoto da bidiyon nata ke da wuya, ya fara tayar da kura a kafofin sada zumunta, inda zuwa lokacin da muke wannan labari, mutum sama da 11,000 ke tattaunawa a kan maudu’in.

Aisha Buhari, wadda aka daina jin duriyarya sosai a kafofin sada zumunta ta bullo da sabon salon ne a daidai lokacin da ta kaddamar da Sashen Mata na Yakin Neman Zaben Tinubu a 2023, wanda kuma take jagoranta.

Ganin hotunan kunshin nata ya sa wasu ke masa fassara da cewa ya nuna 8 + 8 — wato Tinubu zai yi shekara takwas bayan shekara takwas na mijinta, Shugaba Buhari mai ci.

A shafinta na Instagram, Aisha Buhari ta wallafa hotunan taron yakin neman zaben Tinubu da ta kaddamar a Ilori, Jihar Kwara  wanda a cikin hotunan aka gan ta da wasu mata ’yan Jam’iyyar APC sun yi wannan kunshi a tafin hannunsu kuma suna bayyanawa.

Tuni dai kafofin watsa labarai ke ta yin labari a kan sabon salon yakin neman zaben.

Hadimar matar shugaban kasar, Lauretta Onochie da sauran masu amfani da Twitter sun wallafa hotunan a shafukansu.