Gwamnoni ke daukar nauyin ‘yan bangar siyasa a wurin tarukan – Sufeto Janar

0
124

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Baba, ya ce binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa wasu gwamnoni ne ke daukar nauyin ‘yan bangar siyasa domin kawo cikas ga yakin neman zaben abokan takarar su a Jihohinsu.

IGP ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi ga daukacin jam’iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki a harkar zaben.

IGP, wanda bai ambaci sunan wani gwamna ba a cikin jawabin nasa, ya bayyana cewa kawo yanzu, an samu rahotannin tashe-tashen hankula 52 na siyasa tun bayan fara yakin neman zaben 2023.

Yayi gargadin cewa ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen magance wannan matsala da ke kunno kai, ya gargadi ‘yan siyasa da su kaurace wa wannan mummunar dabi’a domin hakan na iya haifar da matsala a zabe mai zuwa.