Qatar 2022: Darajar kofin kwallon kafa na duniya

0
117

Kololuwar burin kowane dan kwallo bai wuce ganin kasarsa ta daga Kofin duniya ba, wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) take sakawa bayan duk wasu shekaru domin kasashe su fafata a samu gwarzo.

Sai dai tun daga lokacin da aka fara buga gasar a shekarar 1930 ya zuwa yanzu, kasashe takwas ne kacal suka taba lashe kofin, mai dimbin tarihi mafi daraja a duniyar kwallon kafa.

Takaitaccen tarihin kofin

An sanya wa kofin sunan Shugaban FIFA na wancan lokacin, Jule Rimnet, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya Gasar Kofin Duniya ta farko a 1930. Tun daga lokacin, kofin ya zama wata alama ta kwallon kafa a duniya.

Wani gursumeti dan asalin kasar Faransa mai suna Abel Lafleur ne ya fara kera kofin, wanda jikinsa zinare da azurfa ne.

Kofin na wancan lokacin dai yana da nauyin kilogiram 3.8, da kuma tsawon santimita 35.

Darajar kofin a wancan lokacin ta kai Dalar Amurka 5,000, amma akan kara darajar bayan kowane shekara hudu da ake sake buga gasar.

A baya dai, tun da aka fara gasar, akan ba da kwafin kofin ne ga kasashen da suka lashe, inda FIFA take ajiye na ainihin a wajenta.

A 1970, lokacin da kasar Brazil ta lashe kofin a karo na uku, aka ba ta damar ajiye na ainihin a hannunta.

Yaya darajar kofin na yanzu take?

Daga bisani FIFA ta yi wa dokokinta garambawul, inda ta ce daga yanzu, ko sau nawa kasa za ta lashe kofin duniya, hukumar ce za ta ajiye kofin na ainihi, ita kuma kasar kwafin na ainihin za a ba ta.

A cewar jaridar USA Today ta kasar Amurka, darajar kofin duniya na FIFA ta kai Dalar Amurka miliyan 20, yayin da wasu ke hasashen zai iya fin hakan.

Waye ya kera kofin Qatar 2022?

Kofin da za a ba duk kasar da ta lashe shi a gasar da za a buga kwanan nan a kasar Qatar, wani dan kasar Italiya mai suna Silvio Gazzaniga ne ya kera shi a shekarar 1974.

A kan ba da kofin ne ga duk kasar da ta lashe shi a karshen gasar da ake yi duk bayan shekara hudu.

Yaya fasalin kofin yake?

Kofin na yanzu yana da tsawon santimita 36.5, kuma nauyin kilo 18 (kaso 75) na kofin zinare ne wanda darajarsa ta kai Dala 250,000.

Yawan zinaren da aka yi amfani da shi wajen kera kofin, musamman wanda aka yi amfani da shi a gasara 2018 ya sa ya zama daya daga cikin wadanda suka fi daraja a tarihin duniyar wasanni.

A halin yanzu dai ba a yi wa kofin wani canji na ku-zo-ku-gani ba, amma ana sa ran ganin an inganta shi a gasar 2022.