Ukraine ce ta harbo mana makami mai linzami – Gwamnatin Poland

0
133

Gwamnatin Poland da Kungiyar Tsaro ta NATO sun ce mai yiwuwa fashewar wani makami mai linzami da aka samu a kasar na tsaron sararin samaniyar Ukraine ne.

Sai dai sun ce Ukraine din ta harbo makamin ne a kokarin kare kanta daga harin da Rasha ta so kai wa kan wani gini na al’ummarta, saboda haka Moscow za a zargi alhakin harin saboda ita ta fara takalar yakin da ake yi tsakaninsu.

Mutum biyu ne aka samu rahoton mutuwarsu sakamakon fashewar makamin mai linzami a wani kauye da ke Poland wanda ya yi iyaka da kasar Ukraine.

Da yake jawabi a ranar Talata, Shugaba Andrzey Duda ya ce makamin samfurin kasar Rasha ne, sai dai ya kara da cewar har a zuwa wannan lokacin babu kwakwarar shaida akan wanda ya harbo shi, amma mun fara bincike.