Barazanar kotu: Madagwal ya ba Sarkin waka hakuri

0
152
Fitaccen jarumin barkwanci, Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal, ya ba Naziru Sarkin Waka hakuri kan sabanin da su ka samu da har ta kai an fara barazanar zuwa kotu.

Ban hakurin na kunshe ne a cikin wani bidiyo da Madagwal ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.

A cikin bidiyon mai tsawon minti 14:50,  Madagwal ya yi dogon jawabi yana mai neman gafarar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.

Madagwal ya kuma roki Naziru Sarkin Waka da ya yafe masa a bisa sakin wasu sakonni na murya da ya yi kan wata sa-in sa da suka yi ta hanyar aika wa junansu sakon muryoyi a manhajar WhatsApp.

Madagwal wanda ya bayyana nadamar abin da ya aikata na yayata muryar Sarkin Wakar, inda ya danganta lamarin da “aikin fushi”.

A farkon makon nan ne Naziru Sarkin Waka ya yi ikirarin gurfanar da jarumin a gaban kotu sakamakon wani kazafi da ya ce masa na cewa, an ba su miliyan 20 amma Nazirun ya ba shi naira dubu hamsin kacal.

Jarumin barkwancin ya furta haka ne a wani sautin muryarsa da aka dauka a yayin da suke cacar baki tsakaninsa da wani mai suna Mazaje.

A cewar Naziru, ya yi magana da Madagwala ta WhatsApp, inda suka yi sa-in-sa shi kuma Madagwal din ya yada sautin hirar da suka yi.