Home Labarai Haaland ba zai buga wa Norway wasan sada zumunta ranar alhamis ba

Haaland ba zai buga wa Norway wasan sada zumunta ranar alhamis ba

0
125

Dan wasan Manchester City, Erling Haaland ba zai yi wa Norway wasan sada zumunta ba da Jamhuriyar Ireland a Dublin ranar Alhamis.

An sa ran Haaland zai buga fafatawar da ta kai ‘yan kallo sun sayi tikiti mutum 45,000, domin ganin mai taka leda a Etihad.

A karshen mako hukumar kwallon kafa ta Norway ta sanar cewar Haaland da mai tsaron raga Jacob Karlstrom ba za su yi wasan da za a kara a Dublin ba.

To sai dai hukumar ta sanar cewar dan kwallon Manchester City zai murmure ya kuma buga mata daya wasan sada zumunta da Finland ranar Lahadi.

Haaland shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Premier League, wanda ya ci 18 a raga kawo yanzu.

Haaland bai buga wasu wasannin ba a watan jiya, bayan da ya jinyar rauni a kafa.

Sai dai ya yi wasan Premier League ranar Asabar da Brentford ta ci City 2-1 a Etihad.

Kafin nan ya ci kwallo a karawar da City ta yi nasara 2-1 a kan Fulham a dai babbar gasar tamaula ta Ingila.