Air Peace ya dakatar da jigila zuwa Dubai saboda hana ‘yan Najeriya biza

0
104
Kamfanin Jiragen Sama na Air Peace ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), saboda hana ’yan Najeriya biza.

Aminiya ta ruwaito yadda hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa suka sanya dokar hana ‘yan Najeriya biza makonni uku da suka gabata.

Tun da farko dai kamfanin dakon kaya na Emirates, ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa, saboda rashin iya mayar da kudaden tikitin baya ga raguwar fasinjojin da suka yi yunkurin zuwa Dubai.

Kamfanin na Air Peace, ya ce zai dakatar da aiki daga ranar Talata, 22 ga Nuwamban 2022, har sai lokacin da ya fitar da sabuwar sanarwa.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce, “Hakan ya biyo bayan ci gaba da rashin bai wa matafiya ‘yan Najeriya biza da Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi da kuma matsalolin da ke biyo baya.

“Air Peace yana aiki da Hadaddiyar Daular Larabawa kan dokar hana tafiye-tafiye na kasar kwanan nan, amma idan aka yi la’akari da matsalolin da matafiya na Najeriya ke fuskanta wajen shiga kasar, ya zama wajibi mu dakatar da ayyukanmu zuwa wani lokaci. Za mu bayar da sabuwar sanarwa nan gaba.