’Yan ta’addan ISWAP sun kona motoci 22 na masu bayar da agaji a Borno

0
113

’Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun kona motoci akalla guda 20 a cikin wata cibiyar bayar da agaji da ke garin Monguno a jihar Borno bayan sojoji sun fatattake su.

Rahotanni sun ce  maharan na ISWAP sun kai hari garin ne da misalin karfe 1:00 na tsakar dare, inda suka rika harbe-harbe ta kowace kusurwar garin.

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, cewa ’yan ta’addan sun auna ma’aikatan agaji ne dake garin na Monguno.

Majiyar ta ce bayan da aka gano cewa babu ko daya daga cikin ma’aikatan a harabar, kasancewar sun gudu don tserar da rayuwarsu, nan take sai  maharan suka kona motoci 18, galibinsu kirar SUV tare da lalata wasu motoci biyu wadanda akasarinsu na kungiyoyin agajin ne.

’Yan ta’addan sun kuma yi yunkurin tafiya da wasu  motoci kirar Hilux guda uku amma sun gamu da turjiya daga dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai, inda suka yi wa ’yan ta’addan mummunar barna sakamakon artabun da suka yi da su.

A cewarsa, maharan sun yi watsi da motocin  ne yayin da suke musayar wuta da jami’an tsaro na musamman kafin su ja da baya su tsere.

Zagazola ya kuma ce ba a sami asarar rai ba yayin artabun.

Monguno gari ne da ke kusa da yankin Tafkin Chadi a Arewa maso Gabashin Najeriya, kuma ‘yan kungiyar ta ISWAP kan kai hari a garin a wasu lokuta da dama da taimakon masu tallafa musu da bayanai.