Zulum ya sake bude kasuwar shanu ta Gamboru, bayan kwashe shekaru a garkame

0
144

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Asabar ya sake bude babbar kasuwar Shanu ta kasa da kasa ta Gamboru wanda aka rufe sama da shekaru bakwai sakamakon hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar.

Babbar kasuwar wacce take da matsuguni a Gamboru, waje ne da ake gudanar da harkokin kasuwanci sosai a iyakar karamar hukumar Ngala da ke cikin tsakiyar jihar Borno.

Gamboru ta hada iyaka da Jamhuryar Kamaru kuma hanyarta na iya hadawa zuwa N’Djamena babban birnin jamhuriyyar Chad.

Zulum wanda ya kasance a karamar hukumar ta Ngala na tsawon kwanaki biyu domin gudanar da harkokin da suka shafi jin kai, ya sake bude kasuwar ne da rakiyar babban jami’in da ke bada umarni (CO) na bataliyar soji ta 3, Lt. Col. Tolu Adedokun, tare da shugaban karamar hukumar Hon. Mala Tijjani.

Zulum ya jinjina da irin kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da rundunar sojin kasa, ‘yan sanda, hukumar tsaron farin kaya, da sauran bangarorin tsaro ciki har da na masu sa-kai da suka bada tasu gudunmawar wajen tabbatar da dawo da tsaro da zaman lafiya a jihar Borno, wanda hakan ne ya kai ga samun nasarar sake bude kasuwar.