An gurfanar da wani mutum a kotu kan satar tayar babur – Ekiti

0
117

An gurfanar da wani mutum a gaban wata Kotun Majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, kan zargin satar tayar babur.

Bayanan da aka samu sun ce gurfanarwar ta hada har da mai babur din da aka sace wa tayar.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfeta Olumide Bamigbade, ya shaida wa kotun cewa, masu kare kansu sun aikata laifin ne ranar 6 ga Nuwamba a yankin Odo-Ado.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, mai babur din ya ajiye abun hawansa ne a wajen gyara ba tare da sanin mai gyaran ba, wanda hakan ya bai wa wanda ake zargi da satar taya damar aikata laifin.

Jami’in ya kuma shaida wa kotun cewa tayar da aka sace darajarta ta kai N12,000.

Ya ce laifuffukan da aka aikata sun saba wa sassa na 261(a) da 302 na Kundin Dokokin Manyan Laifuffuka na Jihar Ekiti na 2021.

Sai  dai wadanda ake tuhumar, sun musanta zargin da ake yi musu.

Lauyan masu kare kansu, Mista Femi Olarewaju, ya nemi kotun ta bai wa wadanda yake karewa beli, tare da yi wa kotun alkawarin ba za su tsere ba.

Alkalin kotun, Misis Franca Olaiya, ta ba da belin wadanda ake zargin kan kudi N100,000 ga kowannensu da kuma shaida guda-guda, kana ta dage shari’ar zuwa 24 ga Nuwamba.