’Yan daba sun kona ofishin INEC na Ogun

0
114

Wasu ’yan daba da ba a gano su wane ba, sun kona muhimman kayyakin zabe a Ofishin Zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Jihar Ogun.

Shaidu sun bayyana cewa wasu mahara takwas ne suka haura katanga suka shiga harabar suka cinna wa ofishin wuta da wasu katifun da suka jika da man fetur.

Wani mai gadin ofishin da ke Abekuta babban birnin jihar, Azeez Hamzat, ne ya kira ’yan sanda da misalin karfe 1:00 na dare ya sanar da su faruwar lamarin.

Aminiya ta gano yadda gobarar ta cinye dakin taro da na rajistar baki na ofishin, kafin motar kashe gobara ta samu nasarar shawo kan wutar.

Rahotanni dai na nuna wasu kayyakin zabe masu muhimmanci ma sun kone sanadiyar gobarar.

Aminiya ta tuntubi Shugaban INEC na jihar, Niyi Ijalaye, ya kuma tabatar mana da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan sanda na ci gaba da bincike don gano wadanda suka aikata ta’asar.