Kotu ta umarci A.A Zaura ya gurfana a gabanta kan zargin rashawa

0
127

Wata babbar kotu tarayya da ke zamanta a Kano ta umarci ɗan takarar sanata a Kano Ta Tsakiya karkashin inuwar APC, kuma fitaccen ɗan kasuwa, Abdulsalam Abdulkarim-Zaura ya gurfana a gabanta kan zargin rashawar dala miliyan 1.3.

Hukumar EFCC ce ta shigar da kara kan A.A Zaura bayan an zarge shi da samun kuɗaɗen ta hanyar da ba su dace ba.

Alkalin kotun Muhammad Nasir-Yunusa da ya bukaci Zaura ya gurfana a gabansa a ranar 5 ga watan Disamba, ya bada wannan umarni ne bayan sauraron karar da aka shigar kan dan takarar.

Alkali Nasir Yunusa ya ce dole ne a ji daga bakin Zaura kafin a dau mataki na gaba.