Ranar Alhamis za a yi zaben kananan hukumomi a Neja

0
139

Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da ranar Alhamis mai zuwa a matsayin ranar da za a gudanar da zaben Kananan Hukumomi a Jihar Neja.

Sanarwar da ta fito ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ta ce Bello ya ba da hutun ne domin bai wa jama’a damar fita zuwa wajen kada kuri’a.

Sakataren ya ce yayin zaben, kasuwanni da ma’aikatu za su kasance a rufe, sannan za a hana zirga-zirgar ababen hawa amma ban da masu ayyuka na musamman.

A cewar Matane, “Gwamnati na kira ga ‘yan jihar da kowa ya fita ya sauke nauyin da ya rataya a kansa a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamban 2022.

“Wannan lokaci ne da za mu fita mu zabi wakilai da shugabannin da za su jagorance mu a matakin Kananan Hukumomi.”

Sanarwar ta ce, Gwamna Sani Bello ya umarci daukacin hukumomin tsaron jihar da su tabbatar ba a samu wani akasi a yayin zaben ba.

Abubakar Sani Bello, ya ayyana ranar a matsayin ranar hutu a fadin jihar albarkacin zaben.