Mutum 13 sun kone kurmus a hatsarin mota a Kano

0
117

Mutum 13 sun kone kurmus wasu shida sun samu raunuka sakamakon hastarin wata bas din kamfanin Kano Line a Hanyar Gaya zuwa Wudil a Jihar Kano.

Mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan bas din kirar Toyota ta yi taho-mu-gama da wata jif kirar Hyundai ranar Lahadi da dare.

Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) Reshen Jihar Kano, Zubairu Nayi, ya ce bas din mai lamba GML 102 TA, da ta fito daga Gombe ce ta yi karo da jif din.

Ya dora laifin hatsarin a kan gudu fiye da kima, da oba-tekin mai hadari.

Don haka ya yi kira ga direbobi da su daina zarce ka’idar gudun da aka kayyade ko yin oba-tekin mai hadari.