Kotu ta hana PDP shiga takarar Gwamna a Zamfara

0
143

Babbar Kotun Tarayya ta haramta wa Jam’iyyar PDP tsayar da dan Gwamnan Jihar Zamfara a zaben 2023.

A ranar Talata ne alkalin kotun da ke zamanta a Gusau, Mai Shari’a Aminu Bappa, ya yanke hukuncin tare da soke sabon zaben dan takarar gwamnan da PDP ta gudanar.

PDP ta gudanar da sabon zaben dan takarar, wanda Dauda Lawal Dare ya lashe ne, bisa umarnin kotun na watan Satumba.

Rikicin zaben takarar na PDP ya kunno kai ne tun bayan da Dauda Lawal ya lashe wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu da kuri’a 431.

Sauran ’yan takara uku — Abubakar Nakwada, Wadatau Madawaki da Ibrahim Shehu-Gusau — sun janye daga zaben bisa zargin magudi.

Amma baturen zaben, Adamu Maina, ya yi watsi da janyewar tasu, saboda ba su sanar a hukumance ba.

Amma a watan Yuni sauran ’yan takara — Shehu-Gusau, Madawaki da Aliyu Hafiz Muhammad — suka shigar da kara suna kalubalantar sakamakon zaben da Dauda Lawal ya lashe.

Don haka suka bukaci kotun ta soke shi saboda kurakurai da saba Dokar Zabe da kuma magudi da suka ce an tafka.

A watan Satumba alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Bappa ya amsa bukatarsu tare da soke zaben na farko.

Sannan ya ba da umarnin a gudanar da sabo, wanda bayan a gudanar Dauda Lawal Dare ya sake lashewa.

Sai dai kuma a zaman kotun na ranar Talata shi ma ta soke shi tare da bayyana cewa PDP ba za ta tsayar da takarar gwamnan jihar a zaben 2023 ba.