Za a sake gwabzawa tsakanin Madrid da Liverpool a zagaye na 16 na kofin zakarun turai

0
123

Real Madrid mai rike da kambun kofin zakarun Turai za ta sake karawa da Liverpool a gasar cin kofin zakarun Turai a zagaye na 16, kungiyoyin sun fafata a wasan karshe na bara, yayin da PSG za ta kara da Bayern Munich.

Madrid na neman sake lashe kofin Turai karo na 15 wanda za a buga a watan Yuni a Istanbul, bayan da ta ci Liverpool 1-0 a wasan karshe na bara a Paris.

Madrid kuma ta doke Liverpool a wasan karshe na 2018 da aka buga a birnin Kyiv.

Za a yi wasannin zagaye na 16 na farko a ranar 14-15 da 21-22 ga watan Fabrairu, yayin da za a yi wasannin na biyu a ranar 7-8 da 14-15 ga watan Maris.

An shirya buga wasan karshe na lashe gasar a ranar 10 ga watan Yuni a filin wasa na Ataturk Olympics da ke birnin Istanbul.

Ga jerin wasannin zagaye na 16 na gasar zakarun Turai a kasa:

RB Leipzig vs Manchester City

Club Brugge da Benfica

Liverpool vs Real Madrid

AC Milan vs Tottenham Hotspur

Eintracht Frankfurt vs Napoli

Borussia Dortmund vs Chelsea
Inter Milan vs Porto

Paris Saint-Germain vs Bayern Munich.