Rikicin masana’antar kannywood: Jaruma Amal ta nemi kotu ta hana ’yan sanda kama ta

0
142

Fitacciyar jarumar Kannywood, Amal Umar ta nemi Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Miller Road ta hana ’yan sanda kama ta da kuma bincikar ta.

Jarumar ta hannun lauyarta Barista Adama Usman, ta yi karar Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda mai Kula da Shiyya ta Daya, da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, da kuma dan sanda mai bincike a ofishin shiyya ta daya.

Lauyar ta ce jarumar ta yi hakan ne sakamakon zargin da wani saurayinta mai suna Ramadan ya yi mata cin kudin wani abokin kasuwancinsa.

Barista Yusuf Dan Sulaiman ya nemi kotun ta shigar da su cikin wadanda ake kara domin su ne suka shigar da karar saurayin nata a ofishin ’yan sanda shiyya ta daya.

“Wanda nake wakilta mai suna Alhaj Yusuf Adamu ya ba saurayin Amal kudi har Naira miliyan 40 da niyyar za su yi kasuwancin wayoyin hannu.

“Amma har zuwa yanzu babu labarin kasuwancin, don haka muka nemi ya dawo da wadanan kudi lamarin da ya gagara. Hakan ya sa muka nemi ’yan sanda da su shiga maganar.”

Barista Dan Sulaiman ya bayyana cewa, lokacin da aka nemi kudin shi ne Ramadan ya bayyana cewa, ya saya wa budurwarsa Amal motar Naira Miliyan biyar, ya kuma kama mata shago tare da zuba mata kayayyaki na miliyan biyar don yin kasuwanci.

Sannan kuma ya ba mahaifinta Naira miliyan uku don ya biya wani bashi da ake bin sa; Baya ga wasu kudade da ya ce ya tura wa jarumar ta asusun bankinta a lokuta daban-daban.

Aminiya ta gano cewa bayan da ’yan sandan suka sami wadannan bayanai ne, suka kwace motar jaruma Amal tare da ci gaba da bincikar ta kan wadancan kudade.

Alkalin kotun, Mai Sharia Sanusi Ado Ma’aji ya sanya ranar 16 ga watan Nuwamba, 2022 don ci gaba da sauraron shari’ar.