ASUU ta umarci malaman Jami’ar Jos su zauna a gida saboda rashin albashi

0
110

Reshen Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Jos na ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU ta umarci mambobinta su zauna a gida har sai gwamnati ta biya su albashinsu da ta riƙe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban ASUU a jami’ar, Dr Lazarus Maigoro, yana faɗar haka a garin na Jos ranar Juma’a.

Sai dai Maigoro ya ce ba yajin aiki suka shiga ba amma dai an ɗauki matakin ne bayan taron da suka gudanar a ranar Juma’ar sakamakon ƙin biyan su cikakken albashin da gwamnati ta yi na watan Oktoba.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ɓangarorin yarjejeniyar da suka cimma da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabeamila shi ne gwamnati za ta biya kashi 50 cikin 100 na albashin watannin da ta riƙe musu nan take.

“Yanzu da muke magana, albashin kwana 17 kawai aka biya mu na watan Oktoba daga ofishin akanta janar na ƙasa,” a cewarsa.