Kotu ta ba da umarnin kwace kadarorin sanata Ekweremadu

0
103

Wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja, ta ba da umarnin kwace wasu kadarori guda 40 da aka danganta su da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu.

Umarnin kotun na zuwa ne bayan korafin da Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC), ta shigar a kan Ekweremadun.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya kuma bukaci EFCC ta wallafa umarnin kwace kadarorin da kotun ta bayar a jaridun kasa nan da kwanaki bakwai.

Kazalika, Alkalin ya kuma umarci duk masu adawa da hukuncin kwace kadarorin, suna da damar bayyana dalilansu cikin kwana 14 bayan wallafa umarnin kotun a jaridu.

Mai Shari’a Ekwo ya dage shari’ar zuwa ran 5 ga Disamba domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Yanzu haka dai mahukunta na ci gaba da tsare Ekweremadu da matarsa Beatrice, a kasar Birtaniya kan zarge-zarge masu alaka da safarar sassan jikin wani yaro mai suna David Ukpo.