Zan sayar da dukkan matatun mai idan na zama shugaban kasa – Atiku

0
141

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya jaddada shirinsa na sayar da dukkan matatun man Najeriya ga ‘yan kasuwa idan aka zabe shi a shekarar 2023.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da gidan rediyon muryar Amurka (VOA Hausa) a ziyarar da ya kai birnin Washington DC na Amurka.

Ya ce, “Wannan ba sabon abu ba ne, tun shekarun da suka gabata na ce zan sayar da su, domin idan ka ba ’yan kasuwa za su fi sarrafa wadannan matatun.

Dangane da batun satar mai a kudancin Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi alkawarin magance matsalar idan ya zama shugaban kasa.

“Wannan wata matsala ce ta daban da ya kamata mu ga yadda za mu yi amfani da karfin gwamnati wajen dakile ta, domin dole ne a samu hadin kai tsakanin NNPC da jami’an tsaro wadanda ke da alhakin kula da bututun mai,” inji shi.

Najeriya na da matatun mai guda hudu a Kaduna, Warri da Fatakwal, wadanda ba sa aiki yadda ya kamata. Hakan ya sa akasarin tace man da ake amfani da shi a Najeriya ana shigo da su ne daga kasashen waje