‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matar kwamandan NSCDC a jihar Nasarawa

0
121

Wasu ‘yan bindiga sun sace matar babban kwamandan rundunar tattara bayanan sirri ta rundunar tsaro da bayar da agaji ta Nijeriya da aka fi sani da Civil Defence, (NSCDC) a Jihar Nasarawa.

Wakilin jaridar Daily trust ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane dauke da bindigogi kirar AK-47, sun kutsa cikin gidan kwamandan inda suka fara harbe-harbe don tsorata jama’a kafin su tafi da uwargidan ta sa.

An samu labarin harbin kanin Kwamandan wanda kuma ma’aikacin NSCDC ne a lokacin da lamarin ya faru a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa.

Yanzu haka ana jinyarsa a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba da ke garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Lamarin dai kamar yadda aka rawaito, ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 8:30 na dare da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC reshen jihar Nasarawa, Mista Jerry Victor, ya bayyana cewa har yanzu ba a san inda ‘yan bindigar suke ba, kuma basu tuntubi kowa ba.