Adalci ne kadai zai ce ci ‘yan Nijeriya – Lawan da Saraki da Wike

0
132

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da gwamnan jihar Rivers, Ezenwo Nyesom Wike, da wasu fitattun ‘yan Nijeriya sun jaddada muhimmancin hadin kai a Nijeriya, inda suka tabbatar da cewa, adalci ne kadai zai cigaba da hadin kan Kasar.

Shugabannin sun bayyana hakan ne a jiya Laraba a Abuja, yayin da ake gabatar da littafi mai suna, “Foundation of Nigeria’s Unity,” wanda dan majalisar dattawan tarayyar Nijeriya mai wakiltar Cross River ta tsakiya, Farfesa Sandy Onor ya rubuta.

Littafin ya ba da haske kan akidun jagoranci na adalci dangane da ci gaban kasa da hadin kai, baya ga tarihin rayuwar dan majalisar da nasarorin da ya samu a majalisar dattawa da dai sauransu.

A wajen taron, Lawan, wanda shi ne babban bako na musamman, ya ce kamata ya yi shugabanni su fi maida hankali ta hanyar duba batutuwan da ‘yan kasa ke gabatar da koke akansu tun da basu da wasu sama da shugabannin su.