Duk da ambaliyar ruwa, babu barazanar karancin abinci a Najeriya – Minista

0
94

Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbacin cewa duk da ambaliyar ruwan da aka fuskanta a sassan Najeriya a bana, babu barazanar samun karancin abinci a kasar.

Ministan Noma da Raya Karkara, Dokta Mohammad Mahmud ne ya bayar da tabbacin yayin wani taron manema labarai a Abuja kan yiwuwar fuskantar karancin abinci ranar Talata.

Ya kuma ce gwamnatin na matukar kokarin ganin ambaliyar ba ta kawo barazana ga kudurin samar da abinci a kasa ba.

Ya ce, “Gwamnati, ta hanyar shirye-shirye da dama na kokarin tabbatar da cewa ambaliyar ba ta kawo wa harkar samar da abinci kalubale ba.

“Babu wata barazanar karancin abinci a yanzu haka, kuma Insha Allahu a 2023 ma ba za a same ta ba.

“Muna kuma kokarin ganin mun sake bunkasa, tare da habaka noman rani yadda ya kamata,” inji shi.

Ministan ya kuma ce harkar noma na daya daga cikin abubuwan da suka ta’allaka kai tsaye da yanayi, kuma duk wata annoba da ta shafi kasa za ta iya kawo mata cikas.

“Dukkan wata kasa mai albarkar noma kuma mai barazanar sauyin yanayi kamar Najeriya dole ne ta sha fama da annoba iri-iri, cikinsu har da ambaliyar ruwa da kuma gobarar daji,” inji Minista Muhammad.

Sai dai ya ce Ma’aikatarsa da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an raba wani tallafin da zai taimaka wa wadanda iftila’in ya shafa su rage radadin ambaliyar.

Jihohi da dama ne a Najeriya suka fuskanci mummunar annobar ambaliyar ruwa a daminar bana, wacce ta janyo asarar rayuka da ta dukiyoyi, ciki har da ta gonaki da amfanin gona.