Buhari ba zai iya tafiyar da Najeriya daga Birtaniya ba – Edwin Clark

0
86

Wani dattijon jiha kuma kwamishinan yada labarai na jamhuriya ta farko, Edwin Clark, a ranar Talata, ya caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan tashinsa zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya domin jinya ba tare da mika mulki ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba.

“Ya kamata Buhari ya gaya wa ‘yan Najeriya ciwon da yake fama da shi”, in ji shi.

A cewarsa, ya kamata Buhari ya bi kundin tsarin mulkin kasa kuma ya yi abin da ake bukata kamar yadda ya dace a duniya domin ba zai iya tafiyar da Najeriya daga kasashen waje ba.

Clark, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a Abuja, ya ce a matsayinsa na shugaban kasa, ya kamata ya sanar da ‘yan Nijeriya duk irin ciwon da yake fama da shi.

Ya ce kamata ya yi a tunkari Kotun Koli don neman taswirar abin da Buhari ya ke yi ba tare da ya shaida wa ‘yan Nijeriya cikakkun bayanai kan halin da yake ciki ba.

“Najeriya ta mu ce gaba daya,  Buhari yana daukar ‘yan Najeriya basu san abinda suke. Ba shi da ikon tashi zuwa Landan ba tare da mika mulki ga mataimakin shugaban kasa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

“A shekaru 95, masu irin shekaru na sunga yadda aka tafiyar da mulkin kasar nan sama da shekaru 70. Najeriya na zubar da jini kuma Allah ne kadai ya san adadin kudin masu biyan haraji da shugaban kasa ya kashe kan lafiyar sa. Girman kai ne Buhari ya yi tunanin zai iya mulkin Najeriya daga kasashen waje. Ya kamata ya mika mulki ga Osinbajo,” in ji Clark.