Tukunyar gas ta yi bindiga, ta yi ajalin wata mata a kwara

0
123

Fashewar tukunyar iskar gas ta kashe wata mata a Unguwar Tabernacle, Garage Egbe a karamar hukumar Omu-aran Irepodun a Jihar Kwara.

Leadership Hausa ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 10:35 na safe a lokacin da take kokarin dafawa iyalinta abinci.

‘Yan kwana-kwana sun iya shawo kan lamarin kan lokaci tare da ceto mijin wanda abin ya shafa wanda shi ma ya makale a lokacin da gobarar ta tashi.

Rahotanni sun ce wuraren ginin da gobarar ta shafa sun hada da dakin zama da kicin da kuma wurin cin abinci.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bukaci jama’a musamman mata da su je su koyi amfani da iskar gas din girki.