Bankin CBN da NIRSAL sun soma kwato bashin da suka bayar

0
91

Babban Bankin Najeriya CBN da bankin masu karamin karfi na NIRSAL sun soma kwato bashin da suka bayar ta hanyar dibar kudin kai tsaye a asusun ajiyar mutane.

Hakan ta bayyana ne a yayin da a ranar Juma’a mutane da yawa wadanda suka karbi bashin suka soma samun sakon kwasar kudi daga asusun ajiyarsu na banki, ta wayoyin hannunsu.

Ta hanyar amfani da tsarin GSI, bankin na iya zuwa kowanne banki da wadanda suka ci bashin suke da ajiya su kwashe.

Wata mai suna Lizzy Atte a hirar ta da The Nation ta koka bisa yadda banki ya kwashe kudin da ke cikin asusun ajiyar ’ya’yanta, ya bar mata N657.14, ta wannan hanyar.

Shi kuwa Mista Kuma, kokawa ya yi da yadda bankin yake kwashe duk kudin da ke asusun ajiyar mutum har sai ya gama biyan bashinsu, a wannan matsanancin halin da ake ciki a kasar.

Wadanda suka ci gajiyar bashin bankin NIRSAL karkashin tsarin ‘COVID-19 TCF’ da ‘AGSMEIS’ da kuma ‘Anchor Borrowers Programme’ ne ta shafa.

“Duk wanda ya ci bashin mu sai ya biya, domin muna da BVN din kowa, kuma za mu yi amfani da tsarin GSI don karbo kudadenmu,” in ji Darktan Kudi na CBN, Mista Philip Yila.

An dade da sanar da cewa bankin zai soma daukar mataki, amma shiru, sai yanzu.