Turkiya zata bawa Najeriya jiragen sama masu saukar ungulu

0
92

Jakadan  Turkiya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce nan ba da dadewa ba jiragen yaki marasa matuka da jirage masu saukar ungulu daga Turkiyya za su isa Najeriya.

Jakadan Turkiya a Najeriya ya bayyana tallafin tsaro da Turkiya ke baiwa Najeriya a matsayin wata nasara daga yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da kasashen biyu suka kulla a shekarar 2021.

Ya kara da cewa, Turkiya na shirin baiwa Najeriya duk wani nau’i na tallafi a kokarinta na dakile barazanar tsaro ta hanyar bada horo a bangaren gogewarta da fasaharta.

Kwangilolin tsaro da aka rattabawa hannu a tsakanin kasashenmu a bara na da matukar tasiri.

A cewar Jakadan Turkiya a Najeriya ,  ya na mai alfaharin sanar da cewa, wasu dandali guda biyu na masana’antun tsaron Turkiya, Bayraktar (TB-2) jirage marasa matuki da kuma (T-149) ATAK masu saukar ungulu za su isa Najeriya.

Jakadan Turkiya a Najeriya  ya ce sabbin kayayyakin kariya na Turkiyya za su taimaka wa kokarin gwamnatin Najeriya tare da bayar da gudummawa sosai ga zaman lafiya, wadata da tsaron ‘yan Najeriya.

Ya ce gwamnatin Turkiyya na kuma sa ran gwamnatin Najeriyar za ta mayar da martanin da suka dace kan harakokin tsaro ta hanyar daukar matakan da suka dace wajen yaki da yan ta’adda a Najeriya.

Dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, Bayraktar ya ce yana matukar alfahari da cewa 2021 da 2022 sun kasance wani babban ci gaba a dangantakar da ke tsakanin Turkiya da Najeriya.

Ya ce, a halin da ake ciki na karuwar huldar kasuwanci a yanzu, yana da yakinin cewa nan ba da jimawa ba Turkiya za ta cimma burin da ta sa a gaba na dala biliyan 5 na hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Karamin ministan harakokin wajen Najeriya, Ambassador Zubairu Dada, ya ce Najeriya da Turkiya sun samu ci gaba a fanin kasuwanci tun bayan ziyarar manyan jami’an kasashen biyu a shekarar 2021.