Kungiyar ‘yan jarida ta raba gari da gwamnatin jihar Yobe

0
107

Kungiyar ‘Yan Jarida Manema Labaru a Jihar Yobe, sun  bayyana daukar matakin raba gari da gwamnatin jihar ta hanyar kauracewa dukar dukkan labaran aikace-aikacen gwamnatin jihar.

Kungiyar, a sanarwar bayan taron gaggawa wanda ta gudanar a ranar Jumma’a, 28 ga watan Oktoba, 2022- mai dauke da sa hannun Shugabanta da Sakatare; Ahmad I. Abba da Micheal Oshomah, sun bayyana daukar matakin sakamakon cin zarafin da jami’an tsaron gidan gwamnati ke yi wa mambobinta.

Kungiyar ta ce ci matakin ya zo ne sakamakon tursasawa tare da cin zarafin da jami’an tsaron gidan gwamnati ke yi wa mambobinta da rashin kallon kimar da gwamnatin jihar ke nuna wa mambobinta.

“Saboda a matsayinmu na daya daga cikin ginshikai hudu a mulkin dimukuradiyya, bangaren da ke aikin sanar da al’umma dukkan abubuwan da ke faruwa a Jihar Yobe.”

“Wanda babban abin takaici ne, ace yau sama da shekara daya amma babu dan jarida a jihar da yayi fira kai tsaye da Gwamna Mai Mala Buni, sannan wannan Kungiyar ba ta taba samun wata gayyata a hukumance daga mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Mamman Muhammed ba, kamar yadda aka saba yi a baya.”

“Wannan ya haifar da mummunan gibi kuma yayi tasiri ga ayyukan wakilan jaridun Nijeriya daban-daban wadanda ke aiki a jihar Yobe.”

“Wanda ya toshewa dukan ‘yan jaridu masu aikin yada labaru samun duk wata damar kaiwa ga Gwamna Mai Mala Buni.”

“Saboda irin yadda wannan abin takaici ke ci gaba da gudana a karkace, kuma duk da cewa tarihi, Gwamna ya taba rike shugaban kwamitin riko a jam’iyyar APC na kasa, inda ya shafe sama da shekaru 3 ya na ganawa da manema labarai a Abuja, da sauran sassan kasar nan, amma ya kasa ya tattauna da yan jaridu a jiharsa, duk da yadda al’ummar jihar suke kewar sanin manufofin gwamnatinsa, tsare-tsare tare da ayyukan da ya aiwatar a cikin wadannan shekaru da yayi a matsayin Gwamnan jihar.”

“Wanda hakan ya jawo kungiyar ta yanke shawarar cewa ilahirin mambobinta za su daina daukar duk wani labari ko sanarwar manema labaru wanda gwamnatin jihar Yobe ta fitar har sai abin da hali yayi.”

“Haka kuma, mambobin wannan Kungiyar suna kira ga shugabannin hukumomin tsaro a jihar Yobe da su wayar da kan jami’ansu su dena cin zarafin kafafen yada labarai.”

“Sannan kuma, mambobin wannan Kungiyar ta ga cewa ya zama dole ta dauki wannan muhimmin mataki a daidai wannan gaba, domin jawo hankalin dukkan masu ruwa da tsaki da hukumomin da suka dace, saboda su dauki kwakkwaran matakin da ya dace tare da magance matsaloli da barazanar da manema labaru ke fuskanta a jihar Yobe don gyara su cikin tsanaki.”

“A karshe, muna sake nanata cewa yan jarida masu aikin yada labaru a jihar Yobe suna sanar da jama’a tare da gwamnatin jihar Yobe cewa basu dauki wannan matakin domin ra’ayin kansu ba, face kawai sai don kasancewarsu a matsayin su na daga cikin ginshikan da ke taimakon ci gaba da dorewar mulkin dimokuradiyyar kasarmu Nijeriya.”

“Har ila yau, yana da mahimmanci a lura cewa babban zabe mai zuwa yana da matukar muhimmanci a dimokuradiyyar kasarmu Nijeriya, don haka kuskure ne duk wani yunkurin yiwa kafafe yada labaru bita-da-kulli.”