DSS ta musanta kai samame wani gida a Abuja tare da sojojin Amurka

0
91

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya ta yi watsi da labarin da ke cewa jami’anta ƙarƙashin hadin gwiwar sojojin Amurka sun kai samame wani gida a Abuja, babban birnin ƙasar.

Mai magana da yawun hukumar Dr. Peter Afunanya ne ya tabbatar wa kafofin yaɗa labarai wannan batu a ranar Juma’a.

Rahotanni sun fara yaɗuwa a farkon wannan makon cewa jami’an DSS da sojojin Amurkan sun kai samamen ne wani gida a unguwar Lugbe inda suka kama wasu mutane da ake zargin ƴan Boko Haram ne tare da abubuwan fashewa da dama.

Hakan na zuwa ne bayan da a farkon makon nan Amurkan ta fitar da sanarwa tana gargaɗin cewa akwai yiwuwar za a kai hare-haren ta’addanci a sassan Najeriya musamman Abuja.

Amma tuni gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wannan batu na Amurka tana mai kiran ƴan ƙasar su kwantar da hankulansu.

Sai dai hakan bai hana Amurka ci gaba da kiraye-kirayen ba, tana mai umartar ƴan ƙasarta mazauna Najeriya da su bar ƙasar.

Kafar yaɗa labaran PR Nigeria ta ruwaito Dr Afunanya yana cewa “Ina shaida mkuku cewa babu wani samame da muka kai tare da sojojin Amurka kamar yadda ake yaɗawa.

“Duk da cewa dai mun kai samame wani rukunun gidaje a Abuja tare da sauran hukumomi abokan aiki, to babu dakarun tsaron ƙasashen waje ko ɗaya a ciki,” ya ce.

PR Nigeria ta ce a wani binciken ƙwaf da ta aiwatar kan zargin dakarun ƙasashen waje sun kai samame rukunin gidaje na Trademore, ya gano cewa “babu wasu ƙwararan hujjoji cewa sojojin Amurka sun kama wani a Abuja.