Mai Martaba Sarkin Kano yayi sabbin nade nade a fadarsa

0
80

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya nada Alhaji Bashir Mahe Bashir Wali a matsayin sabon walin kano da Dakta Mansur Mukhtar Adnan a matsayin sabon Sarkin Ban Kano daya daga cikin Masu zabar Sarkin Kano.

Anyi nadin ne a cikin fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yau juma’a.

Da yake jawabi jim kadan bayan nadin, Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya nada Dakta Mansur Mukhtar Adnan sabo da gogewar sa da irin aikace aikacan da yake gudanar a gwamnati.

Ya kuma hori sabin hakiman da su bayar da gudumawar da ta dace wajan munkasa rayuwar alummar masarautar Kano.

Sabin hakiman sun nuna farin cikin su da zabin su da Mai Martaba Sarkin Kano yayi musu kuma ya nada su a matsayin hakiman da zasu bayar da gudumawa a masarautar kano.

Wakilin Gwamnan jihar Kano, Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna da Ministoci da yan majalisun tarayya da na jahoji sun halarci bikin nadin.