Hukumar Kwastam a Apapa ta tara biliyan 790.6bn a wata 9

0
70

Hukumar Kwastam ta Ƙasa, NCS, reshen Apapa, ta ce ta tara Naira biliyan 790.6 tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar 2022.

Kwanturolan, Malanta Yusuf, mai kula da yankin ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jiya Alhamis a Legas.

A cewar Yusuf, wannan ya nuna wani gagarumin ƙari na Naira biliyan 181.5 idan aka kwatanta da Naira biliyan 609 da aka tara a daidai lokacin shekarar 2021, wanda ke nuna karin kashi 29.8 cikin 100.

“Wannan gagarumar nasara ta samu ne saboda jajircewar jami’an mu na ganin an dakile duk wata ɓaraka da ake samu.

“Hakan yana kuma nuni da yadda masu fataucin kaya da masu ruwa da tsaki ke bin ka’idojin ayyuka.

A kan yaki da fasakwauri, Yusuf ya bayyana cewa, ayyukan hana fasakwauri na daya daga cikin abubuwan da rundunar ta mayar da hankali a kai, musamman ma ayyukan wasu ‘yan kasuwa da ba su tuba ba, wadanda a kodayaushe suke neman hanyoyin da za su lalata tsarin hukumar.