Darajar naira ta karu a kasuwar canjin kudi

0
108

Darajar Naira a kasuwar canji ta farfado zuwa 441.25 a kowace Dalar Amurka a hukumance.

A wasu lokuta a ranar Litinin, sai da darajar Dala a kasuwar canji ta fadi zuwa N425 kafin daga karshe ta koma N441.25.

Darajar Naira a kasuwar canjin ta karu zuwa 441.25 daga Naira N439.63 da aka canji Dala a farkon ranar Litinin din.

A lokacin da kasuwar ta tashi a ranar Juma’a, 14 ga Oktoba, 2022, farashin Dala yana N441.38, amma zuwa safiyar Litinin ya kai N439.63.

Kafin tashin kasuwar a ranar Litinin, Dala ta kai N442.50 kafin daga bisani ta tsaya a N441.25.