‘Yan sanda sun damke wani matashi bisa zargin kashe mahaifinsa

0
92

Rundunar ‘yansandan Jihar Legas ta damke wani matashi dan shekara 21, wanda ake zargin ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 a duniya.

Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), a ranar Talata.

Hundeyin ya ce, rundunar ‘yansanda da ke yankin Abule-Egba a jihar ta samu rahoton kisan daga mahaifiyar wanda ake zargin a ranar Asabar.

Ya ce rahoton ya bayyana cewa da misalin karfe 3:40 na safiyar ranar Asabar, wanda ake zargin ya yi amfani da wani abu mai kaifi ya kashe mahaifinsa a dakinsa.

“Mai karar ya kara da cewa a lokacin da ya isa babban asibitin Oke-Odo, likita ya tabbatar da rasuwar marigayin.

“Yansanda sun ziyarci wurin da aka aikata laifin, sannan an kai gawar zuwa dakin ajiye gawa na babban asibitin Isolo domin kara bincike a kan ta.

“An kai wanda ake zargin zuwa sashen binciken kisan gilla na sashen binciken manyan laifuka na jihar, Panti, domin gudanar da bincike,” in ji shi.