Shugabannin kasashen Afrika 11 na taro don sulhunta rikicin siyasar Chadi

0
86

Shugabannin kasashen tsakiyar Afrika 11 sun yi wata tattaunawa a birnin Kinshasa na Jamhuriyyar Congo da nufin lalubo mafita kan shirin mika mulki ga farar hula a Chadi, ganawar da ke zuwa bayan zanga-zangar adawa da ta kai ga mutuwar tarin fararen hula.

Shugaban Congo Felix Tshisekedi kuma shugaban kungiyar ta ECCAS da ke jagorantar taron ya ce manufar haduwar shi ne lalubo hanyoyin magance rikicin da ya tunkaro kasar tun bayan tabbatar da Deby.

Mahamat Idriss Deby wanda mamba ne a kungiyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika ECCAS a baya-bayan nan ne taron majalisar kasa ya amince da nadinsa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe a kasar, lamarin da bai yiwa bangarorin adawa dadi ba.

Taron mambobin na ECCAS na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zanga-zangar masu adawa da mulkin Soja a kasar ta Chadi da ta kai ga kisan mutane 50 ciki har da jami’an tsaron kasar.

A cewar Tshisekedi wajibi ne a daidaita tsakanin gwamnatin rikon kwaryar kasar da al’umma da nufin samun zaman lafiya da dakile duk wata barazana da za ta kai ga bore ko salwantar rayuka har akai ga komawar mulki hannun fararen hula.

Ko a makon jiya sai da kungiyar Tarayyar Afrika AU da takwararta ta EU suka fitar da sanarwar da ke tir ga abin da ya faru a kasar ta Chadi tare da bukatar bayar da cikakken ‘yancin tofa albarkacin baki a Chadin.