Abin da ya sa na ƙi bayyana manufofina – Kwankwaso

0
95

Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a Najeriya ya ce ana ci gaba da tsare-tsare domin kafa kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

Kwankwaso ya ce ya kuma jinkirta bayyana manufofinsa ne domin gudun ‘satar amsa’ daga sauran jam’iyyun siyasa na ƙasar.

Wasu dai na ganin Rabiu Musa Kwankwaso na jan-ƙafa wajen kafa kwamitin yayin da sauran jam’iyyu suka sanar da nasu tare da fara gangamin yaƙin neman zaɓen.

A cewarsa “za mu fito ne da tsari wanda ya banbanta da na sauran ƴan takara.”

Ya ƙara da cewa “Za mu fito da tsarin abin da za mu yi, da kuma yadda za mu aiwatar da shi.”

Ya ƙara da cewa ya shiga dukkanin manyan jam’iyyun ƙasar biyu (APC da PDP) amma ya dawo daga rakiyar su saboda sun gaza samar da manufofin da za su ciyar da ƙasar gaba.