Yanda wani mutum ya fada ruwa saboda an kala masa sharrin sata

0
84

Bidiyon wani mutum ya fada ruwa a jihar Legas ya yadu sosai a shafukan sada zumunta ranar Asabar.

Wata me suna Ngozi Blessing ce ta wallafa hoton bidiyon a shafinta na sada zumunta inda tace lamarin ya farune a gadar Idumota dake jihar Legas din.
Tace mutumin ya yanke shawarar kashe kansa saboda zargin da aka masa na sace kudi masu yawa wanda ya musanta.
Mutane sun yi ta rokonsa akan kada ya fada ruwan amma yaki ya fada, zuwa yanzu dai babu tabbacin ko hukumomi sun samu damar cetoshi.