Dalilin da yasa muka fasa tsige Buhari – Sanatoci

0
75

Sanatocin Najariya na jam’iyyar PDP sun bayyana dalilin da yasa suka fasa tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A baya dai da lamuran rashin tsaro suka munana, sanatocin sun yi ta barazanar tsige shugaban kasar, saidai daga baya an ji shiru.

Ko da jaridar Punch ta tuntubi wasu daga cikin sanatocin, sai suka ce matakan inganta tsaro da shugaban kasar ya daukane yasa suka fasa tsigeshi.

Daya daga cikin sanatocin Senator Gershom Bassey, yace dama bawai tsige shugaban ne a gabansu ba, inganta harkar tsaro ne suke son ayi.