An kaddamar da kungiyar samar da tsarin ci gaban jihar Kano

0
86

Wasu masu kishin Jihar Kano sun kaddamar da wata kungiya mai suna “Kano Charter” wadda za ta dinga bibiya tare da sanya ido a kan bukatun da al’ummar Jihar Kano suke da su na ci gaba da bunkasar tattalin aziki.

A yayin taron kaddamar da kungiyar wanda aka yi a Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) da ke Kano ya samu halartar manyan mutane masu kishin Jihar Kano daga fannoni daban-daban na fadin jihar.

A jawabinsa, Dokta Isa Ahmed, wanda shi ne shugaban gamayyar, ya bayyana cewa wannan sabon tsari ne da aka shigo da shi domin ganin an dora Jihar Kano a kan turba mai dorewa duk da cewa a shekarun baya ma akwai irin wannan gamayyar.

Ya kara da cewa Kano gari ne mai cike da tarin albarkatu daban-daban saboda haka akwai bukatar samun tsari mai inganci wanda zai dora duk shugaban da zai zo a kan tsarin da zai kawo ci gaba mai dorewa a jihar.

Shi ma a yayin da yake jawabinsa, Farfesa Nu’uman Habib Muhammad da ke Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana cewa dole sai an samu shugaban da zai kasance mai cikakkiyar biyayya da girmama tanade-tanaden tsarin mulki na kasa da addini da wanda zai samar da cin gashin kai da bangarorin shari’a da bijro da tsari mai saukin aiwatarwa.

Sannan ya ce Kano tana bukatar samar da hanyoyin kudin shiga da fitar da tsarin kyautata rayuwar al’umma samar da tsarin rage kashe kudaden al’umma da kuma biyayya ga tsare-tsaren kundin mulkin kasa.

Taron ya samu halartar shugaban Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma  (CITAD), Injiniya Yunusa Zakari Ya’u da Prof. Baffa Aliyu Umar da Dokta Gausu Ahmad da Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa da Dokta Bala Muhammad (Adaidaita Sahu) da Dokta Dalhatu Sani Yola da Farouk Lawal Yola da Nasidi Abdullahi da Ibrahim Ado Kurawa da Farouk Ibrahim Mukhtar da Umar Muhammad Jalo da Ibrahim Sadauki Kabara da Aliyu Isma’il diso da Tafada A. Babba da Ummi Tanko Yakasai da Amina Aminu Dantata da Auwalu Muhammad Umar da Nura Shafi’u da kuma Idris Makama Unguwar Gini da sauransu.