Dan shekara hudu ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga a Yobe

0
92

An kubutar da wani yaro dan shekara hudu mai suna Muktar Adamu a unguwar Nahuta da ke karamar hukumar Potiskum a Jihar Yobe bayan an yi garkuwa da shi a makon jiya.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da aikin ceton ne tare da goyon bayan al’umma da kuma jami’an tsaro daga yankin.

An kuma kama wasu mutane hudu da ake zargin sun yi garkuwa da karamin yaron ne a ranar Juma’ar da ta gabata a unguwar Yindiski da ke garin Potiskum.

Wadanda ake zargin an ce suna hannun ‘yansanda a Potiskum domin ci gaba da bincike.

Daya daga cikin ‘yan unguwar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun da farko masu garkuwa sun yi niyyar sace mahaifin yaron mai shekaru hudu, Malam Adamu, amma shirin nasu ya ci tura, don haka sai suka tafi da dansa.

A halin da ake ciki, kokarin tattaunawa da kakakin ‘yansandan Jihar Yobe kan lamarin ya ci tura.