Har yanzu ina son mijina na boko haram inji ‘yar Chibok da aka ceto

0
102

Daya daga cikin ‘yan matan da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su kwanan nan, Jinka Yama, ta ce a baya-bayan nan tana son haduwa da mijinta na Boko Haram inda ta dage cewa har yanzu tana sonsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya labarta cewa, Yama na son mijin nata ya ajiye makamansa ya mika wuya ga sojojin Najeriya domin burinta na sake haduwa da shi ya zama gaskiya.

Yama ta shaida wa manema labarai a hedikwatar Operation Hadin Kai (OPHK) cewa har yanzu tana kewar mijin ta na uku, Usman wanda shi ne babba ga ‘ya’yanta biyu guda uku.

Yama ta shaida wa manema labarai a hedikwatar Operation Hadin Kai (OPHK) cewa har yanzu tana kewar mijin ta na uku, Usman wanda shi ne baba ga ‘ya’yanta biyu guda uku.