Gwamnati da al’ummar Kano sun bayyana kaɗuwa da rasuwar yan majalisar dokokin jihar biyu a rana guda

0
8

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kaɗuwa da rasuwar ’yan majalisar dokokin jihar biyu a rana guda sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya ce rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji, dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Birni kuma Shugaban Kwamitin Alhazai, da kuma Hon. Aminu Sa’adu na Karamar Hukumar Ungoggo, Shugaban Kwamitin Kasafi, ta girgiza gwamnati da al’ummar jihar baki ɗaya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce mutuwar ’yan majalisar biyu a lokaci ɗaya ta jefa jihar Kano cikin alhini, inda ya bayyana hakan a matsayin wani lokaci mai cike da bakin ciki a tarihin jihar.

Idan za’a iya tunawa Hon. Aminu Sa’adu Ungogo, ne ya fara rasuwa da yammacin ranar Laraba bayan kamuwa da rashin lafiya a marabar majalisar, yayin da Sarki Aliyu Daneji, ya rasu awa guda bayan wannan rasuwa. Daneji ya rasu a asibitin Premier, inda yayi gajeriyar jinya.

Mutuwar ta zamo wani babban abin jimami ga al’ummar Kano, sakamakon cewar ba’a taɓa samun irin wannan rasuwa ba a tarihin Kano.

Daily News 24 Hausa, ta zanta da wasu daga cikin yan uwa da makusantan tsohon ɗan majalisar dokokin ƙaramar hukumar birni Sarki Aliyu Daneji, inda suka bayyana shi a matsayin mutum mai barkwanci da kyautatawa al’umma.

Ɗaya daga cikin waɗanda muka zanta dasu ya ce sunyi wasa da dariya da mamacin kwana guda kafin rasuwar sa, yana mai cewa jikin sa bai nuna gajiyawa sosai ba. Ya kara da cewa sun shafe akalla shekara 30, da Daneji, amma saɓani bai taba shiga tsakanin su ba.

Tuni dai aka gabatar da jana’izar dukkan mamatan bisa koyarwar addinin musulunci, wanda aka binne Aminu Sa’adu Ungogo, a garin Ungogo, a yammacin jiya Laraba, yayin da aka yi jana’izar Sarki Aliyu Daneji, a safiyar Alhamis a Kofar Kudu, dake fadar sarkin Kano, sannan aka binne shi a makabartar Ɗan Dolo.

Jana’izar Daneji, ta samu halartar ɗimbin mutane, da suka ƙunshi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kakakin majalisar dokokin Kano Ismail Falgore, Kwamishinoni, masu bawa gwamna shawara, yan majalisa da sauran al’ummar musulmi.

Muna fatan Allah ya gafarta musu da sauran al’ummar musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here