Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungoggo, Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, ya rasu.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Malam Kamaludeen Sani Shawai, ne ya tabbatar da rasuwar ɗan majalisar a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai.
A cewar sa, marigayin ya kamu da rashin lafiya, jim kaɗan bayan ya isa Majalisar a safiyar yau.
Nan take aka garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwar sa.
A wani cigaban shima ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar birni Sarki Aliyu Daneji, ya rasu, jim kaɗan bayan rasuwar ɗan majalisar na Ungogo, kamar yadda kakakin gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar.


