Tinubu na siyasantar da batun yancin ƙananun hukumomi—Atiku

0
10

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fara aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan ‘yancin kuɗin kananan hukumomi ba tare da ƙarin jinkiri ba.

Atiku, a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta a ranar Laraba, ya zargi Tinubu da siyasantar da hukuncin kotu, yana cewa kin aiwatar da hukuncin wata dabara ce ta siyasa domin matsa wa gwamnonin adawa su shiga jam’iyyar APC.

Ya ce babu buƙatar fitar da umarnin shugaban ƙasa illa kawai Shugaban Ƙasa ya umurci Babban Lauyan Ƙasa da ya aiwatar da hukuncin nan take. A cewar sa, duk wani abu ƙasa da haka gazawar shugabanci ce.

Atiku ya jaddada cewa hukuncin Kotun Ƙoli na ƙarshe ne kuma wajibi ne a bi shi, yana mai cewa kin aiwatar da shi karya kundin tsarin mulki ne da kuma rantsuwar da Shugaban Ƙasa ya yi.

Ya ƙara da cewa hana kananan hukumomi ‘yancin kuɗin su na hana ci gaban al’umma ne a matakin ƙasa, inda hanyoyi ke lalacewa, cibiyoyin lafiya ke rushewa, albashi kuma ba ya samuwa

A ƙarshe, Atiku ya ce Nijeriya na buƙatar shugabanci da ke mutunta doka, ba wanda ke karkatar da ita don amfanin siyasa ba, yana mai gargadin cewa tarihi da ‘yan ƙasa ba za su manta da wannan lamari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here