Ministan Wutar Lantarki Adebayo Adelabu, ya bai wa ’yan ƙasa tabbacin cewa za a cigaba da samunwutar lantarki isashshsiya cikin awanni 24 zuwa 48, bayan raguwar wuta da aka samu a sassan ƙasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manyan masu ruwa da tsaki a ɓangaren wutar lantarki.
A cewar sanarwar da mai bawa ministan shawara kan harkokin sadarwa, Bolaji Tunji, ya fitar, raguwar wutar ta samo asali ne sakamakon fashewar bututun iskar gas na Escravos–Lagos da kuma lalata wasu muhimman bututun gas a yankin Niger Delta.
Yace lamarin ya haifar da ƙarancin iskar gas ga tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da gas, wanda hakan ya rage yawan wutar da ake samarwa a faɗin ƙasa.
Sai dai hukumomi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin gyaran bututun, kuma ana sa ran kammala shi cikin kwana biyu, lamarin da zai ba da damar dawowar iskar gas da kuma ƙaruwar samar da wuta.


