Yan Ta’adda na Amfani da POS Wajen Karɓar Kuɗin Fansa – Gwamnatin Tarayya

0
9

Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa kan yadda ’yan ta’adda ke ƙara ƙirƙiro sabbin dabaru wajen gudanar da ayyukan su, ciki har da amfani da na’urorin POS domin karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka sace.

Daraktan Janar na Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na ƙarshen shekarar 2025 da aka gudanar a hedikwatar cibiyar da ke Abuja.

Ya bayyana cewa biyan kuɗin fansa na ci gaba da zama babbar hanyar samun kuɗi ga ’yan ta’adda, inda yanzu suke amfani da asusun masu POS domin karɓar kuɗin, lamarin da ke sa wahalar gano hanyar da kuɗin ke bi.

A cewar sa, a mafi yawan lokuta, masu garkuwa da mutane kan bai wa iyalan waɗanda suka sace lambar POS, a tura kuɗin zuwa asusun, sannan su je su karɓi kuɗin a hannu, abin da ke wahalar da jami’an tsaro wajen bin sawun kuɗin.

Janar Laka ya ce jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen sa ido kan biyan kuɗin fansa, kama waɗanda ke da hannu a ciki da kuma rusa hanyoyin da ake amfani da su wajen tallafa wa ta’addanci, duk da cewa ba za a iya bayyana cikakkun bayanan ayyukan shirin ba saboda dalilai na tsaro.

Ya kuma tabbatar da cewa an riga an kama mutane da dama tare da gurfanar da su a kotu bisa laifin taimakawa ta’addanci ta hanyar kuɗi, tare da kwato kadarori da aka samu ta haramtacciyar hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here