’Yan Majalisar Wakilai shida daga Jihar Rivers sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
’Yan majalisar da suka sauya sheƙa sun haɗa da Dumnamene Dekor, Cyril Hart Godwin, Solomon Bob, Victor Obuzor, Blessing Amadi da Felix Uche.
An karanta wasiƙun ficewar su a zauren Majalisar Wakilai a ranar Talata, inda Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya sanar da hakan a hukumance.
’Yan majalisar sun bayyana cewa rikicin shugabanci da rabuwar kai da ta daɗe tana addabar jam’iyyar PDP ce ta sa suka kasa cimma burin su na siyasa da na aiki, wanda hakan ya tilasta musu sauya jam’iyya.
Wannan sauyin sheƙar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ’yan majalisa huɗu daga Rivers sun koma APC daga PDP da LP, lamarin da ya ƙara raunana jam’iyyun adawa a jihar.
Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙa a baya akwai Boniface Emerengwa, Awaji-Inombek Abiante da Boma Goodhead daga PDP, sai kuma Manuchim Umezuruike wanda ya fice daga jam’iyyar LP.


