Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ceto wani mutum daga hannun fusatattun mutane, bayan an zarge shi da aikata abin da ya shafi cin zarafin addini a wani otal da ke unguwar Badawa a cikin birnin Kano.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:45 na dare a ranar Lahadi, 21 ga Disamba, 2025, a wani otal mai suna Sarina da ke unguwar Badawa.
Wani masani kan rahotannin harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cewa wasu mutane uku daga unguwar Dorayi ne suka je otal ɗin, inda ake zargin sun shiga domin shan shisha.
Daga cikin su, ana zargin ɗaya mai suna Musa Tasiu ya shiga masallacin otal ɗin, ya lalata ƙofar gilashi, sannan ya ɗauki Alƙur’ani mai girma ya yaga shi.
Bayan faruwar lamarin, mutane da ke cikin otal ɗin sun taru da yawa, inda lamarin ya kusa rikidewa zuwa rikici.
Sai dai jami’an ’yan sanda da ke sintiri a yankin sun gaggauta kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, inda suka ceto mutumin daga hannun jama’a tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Rundunar ’yan sandan ta ce yanzu haka an shawo kan lamarin gaba ɗaya, kuma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.


