Amurka ta dakatar da bawa ƴan Najeriya bizar shiga ƙasar

0
8

Jakadancin ƙasar Amurka da ke Najeriya ya sanar da cewa zai dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya, daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Matakin ya biyo bayan sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, wadda ta bayyana cewa za a taƙaita bayar da biza ga ’yan ƙasashe 19, ciki har da Najeriya, domin kare tsaron ƙasar Amurka.

A cewar sanarwar, dokar za ta fara aiki da misalin ƙarfe 12:01 na dare a ranar 1 ga Janairu, 2026, bisa umarnin shugaban ƙasa mai lamba 10998, wanda ya shafi shigar baki zuwa Amurka.

Jakadancin Amurka a Najeriya ya sake jaddada wannan mataki ta shafinsa na X (Twitter) a daren Litinin.

Sanarwar ta ce dakatarwar ta shafi, bizar yawon buɗe ido, bizar ɗalibai da masu musayar ilimi da bizar zama na dindindin, sai dai wasu kaɗan da aka ware.

Waɗanda aka ware sun haɗa da:

Mutanen da ke fuskantar tsanantawa ta addini ko kabila

Mutanen da ke da fasfo na wata ƙasa da ba ta cikin jerin

Ma’aikatan gwamnatin Amurka masu biza ta musamman 

’Yan wasa da ke halartar manyan gasa

Masu katin zama na dindindin a Amurka

Sauran ƙasashen da dokar ta shafa sun haɗa da Angola, Benin, Senegal, Gambia, Côte d’Ivoire, Tanzania, Venezuela da wasu ƙasashe na Afirka da Amurka ta Tsakiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here